Nuwamba ita ce wata na goma sha ɗaya na kalandar Miladiyya, wadda ake amfani da ita a faɗin duniya. Kalmar “Nuwamba” ta fito ne daga kalmar Latin “novem,” wanda ke nufin “tara,” domin shi ne farkon watan tara na kalandar Romawa.Duk da haka, lokacin da aka gyara kalandar Romawa daga baya da Janairu. aka kara Fabrairu, Nuwamba ya zama wata na goma sha daya. Yawanci watan Nuwamba yana da alaƙa da farkon kaka ko faɗuwa a yankin arewaci, da kuma bazara a yankin kudanci.