Louisville birni ne, da ke a jihar Kentucky, a ƙasar Amurka. Sunan "Louisville" ya fito ne daga Sarki Louis na 16 na Faransa, wanda ya kasance abokin Amurkawa 'yan mulkin mallaka a lokacin yakin juyin juya hali. George Rogers Clark, wanda ya kafa birnin a shekara ta 1778 ne ya sanya sunan birnin don girmama shi.